Yadda Kunne Yaji Lyrics
Yadda kunne yaji haka zuciya ke aunawa
Inda raina da rabona zaki ganewa
Nidake sirrin juna zamuyi boyewa
Ra'ayina kece kikka zamanto tawa
Ki kulamin dakaina ma'ajin sirrina
Hakan shine zai sanyaya ruhina
Wa'adina yazo indai bakya sona
Tunda naji wayansu akanki suke zagina
Kinga tauna sam ba'ayi sai da hakura
Kikira gefenki nazona sarara
Ko’a dan aiki daukeni nakore kura
Nifaba komai kanki kada an min kyara
Ni kawai sonki nake dan zuciya ta harbu
Da ace zakiyi shagwaba nizan miki bambu
Fadamar sanyi kikaso nahada miki lambu
Kanki zan iya danne koda hannu ba kanbu
Tausaya min agaza min kada ki min bore
In Na aiko sakonnin so karda ki share
narasa ki masoyiyata dole na zare
Shi dafinso naki dawuya ataya zan jure
Kalmomin dakike minni nakeyin hadda
A kwakwalwata na ajesu zamar min shaida
Bani inbaka sone baya yin tsada
Nai sabo dake sonki zuciya ya huda
tunani dake kowa tare ya ganmu
Hanta da jini tilas sai anbarmu
Nayi kuka kwakwalwa sonki yake damu
Nazari aure nake ataya zan samu
Babu laifi danni kedai nayi wa kishi
Ko kalli naga wani yanay saina tsane shi
So ya danne ni asa'in dakyar zanai ninshi
Kinji sakona ina fatan daki karbeshi
Kada ki bari ya zamana kuka
Ni masoyi ne kanki kamar nayi hauka
Ki gina min sharudai naki kawai na dauka
kaunarki nake babu dare ba rana
Ajikina nakejin kina saurarena
Abar kaunata kin tsaurata alwashina
mafakar ruhi kaunarki tanata gudana
Kanki dai na zaku daure ki zamo gatana
Ina fatan wataran kikirani habibi
Zanji dadi mai sona ko bayan raina
Koda ace aduniya ba numfashina
Kintuna wanda kikeso yazamo ni daina
Da kin tuna wanda kibeso yazamo nidaina
Da kin tuna wanda kibeso yazamo nidaina
WATCH VIDEO
ABOUT THIS SONG
Release Year : 2020
Album : Yadda Kunne Yaji (Single)
Added By : Farida
SEE ALSO
AUTHOR
HAMISU BREAKER
Nigeria
Hamisu said yusuf, known as Hamisu Breaker a Nigerian musician, Performing Artist, songw ...
YOU MAY ALSO LIKE